Newsletter Help
Change language Hausa

Yadda zaka zama mamba

Become a KPR member, and enjoy cheaper prices immediately. Register here.

Delivery to 24 countries is now much cheaper. Click here to learn about new shipping fees to your country.

Fom na Rijistar Xan Qungiya

Ina so in zama mamban KPR

Bayanai kan zama mamba

Tun daga watan Satumba 2007 za ka iya zama mamban KPR ko da baka magana ko fahimtar yaren Slovakiya.
A shekara ta 2000, mun fara kulaf xinmu a yaren Slovakiya. Tun daga wannan lokaci,muke ta samun qaruwar mambobi musamman daga Slovakiya da Czechiya.
Yanzu za ka amfana da duk wasu amfanunnukan mamban KPR a Slovakiya – ba tare da la’akari da kai ko wanene ba ko kuma wane yare ka ke magana da shi ba.
Muna maraba da kowa daga ko ina a duniya wanda ya ke qaunar shuke-shuke. Hanzata shigowa cikin mu!
Kaico, har yanzu akwai matsala guda: Ba zaka sami damar karanta mujallar ‘yan kulab ta Botanix ba, idan ba ka fahimtar yarukan da ake wallafa mujallar ta Botanix da su ba.
Ta wata fuskar, mai zai hana ka fara taka mujallar da yarenka? Haxa gwiwa da sauran manoman lambu, waxanda suke magana da yare iri xaya, ku fara rubutu ko tattara maqaloli masu ban sha’awa akan aikin lambu, shuke-shuke da sauran su, daga nan sai ku fara taku mujallar ta Botanix a cikin yarenku!
Babu wani tarnaqi ga yinqurinku!
Ta wata fuskar, bayanan da za su iya tasowa musamman domin manoman lambu na Slovak ba lallai ne su dace da manoman da suke qasashe masu zafi ba ko akasin haka, sabo da haka wallafa mujallar Botanix a yaruka daban-daban abu ne mai kyau.

Zama xan qungiyar KPR na Slovakiya.

Me yasa zan zama xan qungiyar KPR?

1. Xan qungiyar KPR na iya bada oda a farashi mai kyau. Ga misali nan a qasa. (Babu iyaka ga odoji.)

Farashinsa ga mambobin KPR Farashinsa ga wanda ba mamba ba %-rangwame
0,50 € 0,70 € 29%
0,70 € 0,90 € 22%
1,00 € 1,50 € 33%
3 € 4 € 25%

2. Duk xan qungiya na iya xaukar samfurin tsaba guda biyar a duk shekara (amma banda kwara da tsabar sikads, da kuma tsabar wasu zavavvun ire-ire) daga Rumbun Ajiye Tsaba da shuke-shuke na KPR. Bugu da qari manbobi sun cancanci ragin 50% na sauran samfuri (madaidaicin farashin samfuri shi ne Yuro 1; to amma manbobin KPR Yuro 0,50 ne kacal).

3. Ana fara aiki akan odar mamban KPR kafin wanda ba mammba ba.

4. Ana ganawa kyauta a yaruka 11 a cikin shekara dangane da raya shuke-shuke

5. Za ka iya amfani da ayyukan Buxaxxen Asusu.

Buxe asusu - Bayani akan Buxaxxen Asusu
Buxaxxen Asusu ita ce hanya mafi sauqin sayayya a KPR. Sai ka fara biyan kuxi kafin ka yi odar komai – duk lokacin da ka ke son yin oda, nan take za’a caji odarka daga ragowar kuxin da ke cikin asusunka. Wannan yana nufin ba sai mun jira ka turo kuxi ba kafin mu fara aiki akan odarka, kuma za’a iya shirya odarka a aiko ta nan take. Za ka iya zuba kuxi a Asusun Ajiyarka a kowane lokaci, ta amfani da hanyoyin biyan da aka yarda da su.
Duk lokacin da ka buqaci zuba kuxi a Buxaxxen Asusunka, ka buga lambarka domin mu sami damar gano dalilan biyan. Daga nan za mu zuba kuxin a Buxaxxen Asusunka da zaran kuxin sun shigo. Babu iyaka akan kuxaxen da za ka iya qarawa a Buxaxxen Asusunka. Zaka iya amfani da ragowar kuxin da ke Buxaxxen Asusunka da zaran kuxin da ka zuba sun shigo.
Idan kana buqatar biyan odar da ka yi ta amfani da ragowar kuxin Buxaxxen Asusunka, kawai sanar da mu da wannan saqo: “A biya oda ta ta amfani da Buxaxxen Asusuna mai lamba XXXXXXX”. Nan take za’a caji odarka kuma a ci gaba da shirye-shiryen aikota da zarar an kammala duk shirye-shirye.
Za ka iya neman a dawo maka da kuxi a Buxaxxen Asusunka. To amma, ka sani za’a caje ka xan wani abu domin dawo maka da kuxin da aka yi. Ba’a cajin komai idan aka dawo maka da kuxi ta hanyar biya ta PayPal; kuma mafi yawan abin da za’a caje ka idan aka dawo maka da kuxi ta hanyar moneybookers.com shi ne Yuro 0,50. Babu cajin kuxi idan aka dawo maka da kuxi ta hanyar bankin qasa a Qasashen Slovakiya da Czeciya. Kada ka yi qasa a gwiwa wajen tuntuvarmu dangane da abin da ya shafi biyan kuxi / sauran hanyoyin biya da suka shafi sauran qasashe. Mun sha alwashin dawo maka da kuxinka cikin Buxaxxen Asusunka a cikin kwana 60 daga lokacin da ka nuna buqatar hakan.
Lura: Yin amfani da Buxaxxen Asusu zai kare ka daga biyan kuxaxe domin aike-aiken kuxaxe. Abin da kawai ka ke buqata shi ne aika kuxi da zaran an buxe maka Buxaxxen Asusu kuma ka dinga biyan odarka daga wannan asusu iya adadin da ka ke da buqata.
Akwai tambayoyi?

6. Idan ododjinka a shekara ta 2010 sun wuce Yuro 80, za ka iya bayar da odar ko wace irin tsaba ko shuka da ta kai qimar Yuro 10 KYAUTA!

7. Ana yin kalo-kalo a duk shekara da kyautukan Yuro 50,30, da kuma 15 domin siyayya tare da mu!...tare da qarin wasu damammaki da zamu dinga sanar da kai.

...and many other advantages regarding which we will keep you informed.

Sharaxin zama mamba

1. Kana da buqatar cike Fom xin rijista don zama mamba kuma ka biya Yuro10 kuxin qungiya na shekara-shekara kafin 31 ga watan Mayu na shekarar zama mamba. Ana yin amfani da kuxin da aka tara wajen gudanar da ayyukan ci gaban KPR a faxin duniya.

Kuxin qungiya na shekarar

( Halaccin zama mamba yana farawa daga 1.10.2018 zuwa 31.12.2019)

Kuxin Shekara-shekara Shekarar farko Sabuntawa a shekarar gaba
10 Euro 5 Euro

2. Zaka iya bayarda oda a qalla sau 2 a kowace shekara daga Garavasar Kulaf. Babu iyaka ga kowace oda.

3. Zaka iya biyan wasu kuxi na sa-kai tare da kuxin rijistarka wanda za’ayi amfani da su wajen gudanar da ayyukan gamayya na KPR a duk faxin duniya.

Kana da sha’awar zama mamban KPR? Ta kwana gidan sauqi! Shigo cikinmu nan take. Kawai cike wannan fom na Rijistar Xan Qungiya.

Fom na Rijistar Xan Qungiya

Ina so in zama mamban KPR


Ka haxa wannan kaya a cikin Baronka ta Siyayya.