Become a KPR member, and enjoy cheaper prices immediately. Register here.
An kafa KPR a shekara ta 2000 a qasar Slovakiya, wani yanki na kasashen turai; tun kafin wannan lokaci, muna samar da ire-ire da kuma shuke-shuke zuwa ga sassan duniya tun daga shekara ta 1998.
Babban burin mu shine haxa kan masu noman lambu na ko wane irin nau’in kaya na duk duniya, domin samar da wani jadawali na dukkanin ire-ire da shuke-shuke (Asusun Ire-ire da Shuke-shuke na KPR) daga duk sassa na duniya.
A halin yanzu, muna da manyan rassa guda shida a (Slovakiya, Czechiya, Astaraliya, Hindiya, Thailand, Afirka ta Kudu da Tanzaniya) da kuma sama da mataimaka da masu tara ire-ire sama da 200 daga duk fadin duniya.
A yau munyi nasarar tara da kuma raba sama da nau’in shuke-shuke 10 000 a sassa daban-daban na duniya.
Idan kana neman wani abu, ka dace da abin da ka ke nema! Bamuyi iqirarin cewa muna da duk shukar da ka ke nema ba, to amma sannu bata hana zuwa, a hankaki a hankali muna samun iri da shuka daya-bayan-daya. Munyi imani cewa ba da daxewa ba zamu samar da (kusan) komai!
Domin sayarwa sama da tsaba 10 000 da kuma shuke-shuke daga duk sassan duniya – kwara, sikads, bishiyoyi da shuke-shuken kasashen waje,shuke-shuke da bishiyoyi masu jure yanayin hunturu, bashiyoyi masu bada ‘ya’ya masu ruwa, shuke-shuken dabbobi masu cin nama, bishiyoyi masu gajeren kwana, bishiyoyi masu dogon kwana, ciyawar ado, kayan marmari da suran su.